ABNA24 : Wasu matasan sun bayyana cewa matukar ba a sako jagoran ‘yan hamayyar ba wanda shi ne fatansu a fagen siyasa, to za su sake komawa kan tituna domin ci gaba da Zanga-zanga.
A yau Litinin ne dai ake tsammanin gabatar da Sonko a gaban kotu domin ya fuskanci shari’a bisa zargin da ake yi masa na yin fyade.
Sonko dan shekaru 46 dai ya tsaya takarar shugabancin kasar a zaben da aka yi a 2019, sai dai ya zo na uku wajen samun yawan kuri’u.
Matsalar da samarin kasar suke fuskanta ta talauci da kuma yadda gwamnatin kasar take ta’ammuli da Corona, su ne muhimman batutuwa da Sonko ya yi amfani da su wajen jawo hankalin samarin kasar.
Har lia yau, ana daukarsa a matsayin babban wanda zai iya kalubalantar shugaba Macky Sall a zaben 2024.
342/